(ABNA24.com) A wani bayani da ya fitar Pirai ministan kasar Iraki Adil Abdul Mahdi ya sanar da kafa dokar tabaci a fadin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar, har sai baba ta gani, sakamakon ci gaba da zanga zangar nuna rashin amincewa da matsalar tattalin arziki da alummar kasar ke ciki,
Sai dai ma’aikatan Asibiti da na filin sauka da tashin jirgin sama, da motocin daukar marasa lafiya da bangren wutar lantarki da masu ziyarar wurare masu tsarki da malamai basu cikin wadanda dokar za ta shafa, kuma tuni aka sanya dokar a lardunan Nasiriya, Amara da kuma garin hilla.
kafin sanar da wannan dokar sai da pira ministan ya yi ganawar gaggawa da majalisar tsaron kasa domin daukar matakin daya dace wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane, zanga- zangar ta barke ne tun a ranar talata da ta gabata domin nuna rashin amincewa da matsatsin tattalin arziki da rashin aikin yi dake addabar alummar kasar.
/129
5 Oktoba 2019 - 04:44
Lambar labari: 980249
A wani bayani da ya fitar Pirai ministan kasar Iraki Adil Abdul Mahdi ya sanar da kafa dokar tabaci a fadin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar, har sai baba ta gani, sakamakon ci gaba da zanga zangar nuna rashin amincewa da matsalar tattalin arziki da alummar kasar ke ciki,